Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Sai sarkin fada ya raɗa musu sababbin sunaye, ga Daniyel ya raɗa masa Belteshazar; ga Hananiya ya raɗa masa Shadrak; ga Mishayel ya raɗa masa Meshak; ga Azariya kuma ya raɗa masa Abednego.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 1:7
13 Iomraidhean Croise  

Fir'auna kuwa ya sa wa Yusufu suna, Zafenat-faneya. Ya kuma aurar masa da Asenat 'yar Fotifera, firist na On. Yusufu kuwa ya fita rangadin ƙasar Masar.


Sai Fir'auna-neko ya sarautar da Eliyakim ɗan Yosiya a matsayin tsohonsa. Ya sāke masa suna ya sa masa suna Yehoyakim. Ya ɗauki Yehowahaz ya tafi da shi Masar, can ya mutu.


Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya naɗa Mattaniya ɗan'uwan tsohon Yekoniya sarki a maimakon Yekoniya sa'an nan ya ba shi suna Zadakiya.


Da sarki ya yi magana da su, sai ya tarar a cikinsu duka, ba wani kamar Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya. Don haka aka maishe su 'yan majalisar sarki.


Sa'an nan Sarkin Babila ya umarci sarkin fādarsa, Ashfenaz, ya zaɓo masa waɗansu samari daga cikin Yahudawa, waɗanda suke daga gidan sarauta, da kuma daga gidan manya,


A shekara ta uku ta sarautar Sairus Sarkin Farisa, sai aka aiko da saƙo wurin Daniyel, wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar. Saƙon kuwa gaskiya ne, ya shafi zancen yaƙi, Daniyel kuwa ya fahimci saƙon.


Sarki kuwa ya ce wa Daniyel, mai suna Belteshazzar, “Ka iya faɗa mini mafarkin duk da fassararsa?”


Daniyel kuwa ya roƙi sarki ya naɗa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego su zama masu kula da harkokin lardin Babila, amma Daniyel yana fādar sarki.


Sa'ad da nake kwance a gādona, sai na yi mafarki wanda ya tsorata ni. Tunanina da wahayi suka firgitar da ni.


Daga baya sai Daniyel wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, wato irin sunan allahna, yana kuwa da ruhun alloli tsarkaka, ya shigo wurina. Na kuwa faɗa masa mafarkin, na ce,


Yana da ruhun nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma'anar ka-cici-ka-cici, da warware al'amura masu wuya. Shi ne wanda sarki ya laƙaba wa suna Belteshazzar. Don haka sai a kirawo maka Daniyel, shi kuwa zai sanar maka da ma'anar.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan