14 Ya yarda da abin da Daniyel ya ce, ya kuwa jarraba su har kwana goma ɗin.
14 Sai ya amince da haka ya kuma gwada su har kwana goma.
Sa'an nan ka duba fuskokinmu da na samari waɗanda suke cin abinci irin na sarki. Ka yi da barorinku gwargwadon yadda ka gan mu.”
A ƙarshen kwana goma ɗin, sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki.
Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.