Zabura 98 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 98 Zabura ce. 1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto. 2 Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai. 3 Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu. 4 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi; 5 ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa, 6 tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki. 7 Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta. 8 Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki; 9 bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.