Zabura 87 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 87 Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. 1 Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki. 2 Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub. 3 Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, Sela 4 “Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ” 5 Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.” 6 Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” Sela 7 Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.” |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.