Zabura 82 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 82 Zabura ta Asaf. 1 Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”. 2 “Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela 3 Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya. 4 Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye. 5 “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya. 6 “Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne. 7 Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.” 8 Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.