Zabura 8 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 8 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Zabura ta Dawuda. 1 Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai. 2 Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru. 3 Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu, 4 wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi? 5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma. 6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa, 7 dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji, 8 tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku. 9 Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.