Zabura 57 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 57 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. 1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce. 2 Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka, ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni. 3 Ya aika daga sama ya kuwa cece ni, yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; Sela Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa. 4 Ina tsakiyar zakoki; ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane, mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi, waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi. 5 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya. 6 Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna, damuwa ta sha ƙarfina. Sun haƙa rami a hanyata, amma su kansu suka fāɗa a cikinta. Sela 7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe. 8 Ka farka, raina! Ku farka, garaya da molo! Zan sa safe yă farka. 9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai a cikin mutane. 10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai; amincinka na kaiwa sarari. 11 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.