Zabura 54 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 54 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?” 1 Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka. 2 Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina. 3 Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela 4 Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni. 5 Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su. 6 Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau. 7 Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.