Zabura 53 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 53 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat. Wani maskil na Dawuda. 1 Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa, “Ba Allah.” Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau; babu wani mai aikata abu mai kyau. 2 Allah yana duba daga sama a kan ’ya’yan mutane yă ga ko akwai wani wanda ya gane, wani wanda yake neman Allah. 3 Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace; babu guda da yake aikata abu mai kyau, babu ko ɗaya. 4 Masu aikata mugunta ba sa taɓa koyo? Suna cin mutanena kamar yadda ake cin burodi, ba sa kuma kira ga Allah. 5 Ga shi fa, sun firgita don tsoro, ko da yake babu dalilin tsoro, gama Allah zai watsar da ƙasusuwan masu ƙinsa, za su sha kunya, gama Allah ya ƙi su. 6 Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna! |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.