Zabura 47 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 47 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. 1 Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki. 2 Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya! 3 Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu. 4 Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela 5 Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni. 6 Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai. 7 Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi. 8 Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki. 9 Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.