Zabura 4 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 4 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. 1 Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka, Ya Allahna mai adalci. Ka ba ni sauƙi daga wahalata; ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata. 2 Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya? Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Sela 3 Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa; Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi. 4 Cikin fushinku kada ku yi zunubi; sa’ad da kuke kan gadajenku, ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Sela 5 Ku miƙa hadayun da suka dace ku kuma dogara ga Ubangiji. 6 Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?” Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji. 7 Ka cika zuciyata da farin ciki sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa. 8 Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.