Zabura 3 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 3 Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. 1 Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni! 2 Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela 3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. 4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela 5 Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. 6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba. 7 Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye. 8 Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.