Zabura 29 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 29 Zabura ta Dawuda. 1 Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa. 2 Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa. 3 Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye. 4 Muryar Ubangiji mai iko ce; muryar Ubangiji da girma take. 5 Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu. 6 Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, Siriyon kuma kamar ɗan jakin jeji. 7 Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya. 8 Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh. 9 Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!” 10 Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada. 11 Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.