Zabura 26 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 26 Ta Dawuda. 1 Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba. 2 Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina; 3 gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka. 4 Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya; 5 na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye. 6 Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji, 7 ina shelar yabonka da ƙarfi ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki. 8 Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune. 9 Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi raina tare da masu son yin kisankai 10 waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu, waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci. 11 Amma na yi rayuwa marar zargi; ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai. 12 Ƙafafuna suna tsaye daram; cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.