Zabura 20 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 20 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. 1 Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka. 2 Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona. 3 Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Sela 4 Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara. 5 Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka. 6 Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa. 7 Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu. 8 Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram. 9 Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira! |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.