Zabura 149 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 149 1 Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka. 2 Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu. 3 Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya. 4 Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto. 5 Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu. 6 Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu, 7 don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane, 8 don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe, 9 don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.