Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Zabura 143 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Zabura 143
Zabura ta Dawuda.

1 Ya Ubangiji, ka ji addu’ata, ka saurari kukata don neman jinƙai; cikin amincinka da adalcinka ka amsa mini.

2 Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a, gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.

3 Abokin gāba yana fafarata, ya murƙushe ni har ƙasa; ya sa ina zama a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu tun tuni.

4 Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina zuciyata ta damu ƙwarai.

5 Na tuna da kwanakin baya na yi tunani a kan dukan ayyukanka na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.

6 Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela

7 Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji; ƙarfina ya ƙare. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.

8 Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa, gama na sa zuciyata a gare ka. Ka nuna mini hanyar da zan bi, gama a gare ka na miƙa raina.

9 Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka.

10 Ka koya mini in yi nufinka, gama kai ne Allahna; bari nagarin Ruhunka yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.

11 Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina; a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.

12 A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana; ka hallaka dukan maƙiyana, gama ni bawanka ne.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
Lean sinn:



Sanasan