Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Zabura 141 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Zabura 141
Zabura ta Dawuda.

1 Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira.

2 Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa; bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.

3 Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana.

4 Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu, ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka tare da mutane masu aikata mugunta; kada ka bari in ci abincinsu.

5 Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne; bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina. Kaina ba zai ƙi shi ba, duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.

6 Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne.

7 Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa, haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.”

8 Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka; a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.

9 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini, daga tarkon da mugaye suka sa.

10 Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu, amma bari ni in zo in wuce lafiya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
Lean sinn:



Sanasan