Zabura 128 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 128 Waƙar haurawa. 1 Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa. 2 Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka. 3 Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka. 4 Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji. 5 Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima, 6 bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.