Zabura 124 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 124 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. 1 Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce, 2 da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana, 3 sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai; 4 da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu. 5 Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf. 6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba. 7 Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira. 8 Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.