Zabura 122 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 122 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. 1 Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.” 2 Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima. 3 An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda. 4 A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila. 5 A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda. 6 Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya. 7 Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.” 8 Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.” 9 Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.