Zabura 114 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 114 1 Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe, 2 Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa. 3 Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya; 4 duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki. 5 Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya, 6 ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki? 7 Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub, 8 wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.