Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Mika 3 - Sabon Rai Don Kowa 2020


An Tsawata wa Shugabanni da Annabawa

1 Sa’an nan na ce, “Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila. Ya kamata ku san shari’a,

2 ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta, ku da kuke feɗe mutanena kuke tuge nama daga ƙasusuwansu;

3 ku da kuke cin naman mutanena, ku feɗe fatar jikinsu kuke kakkarya ƙasusuwansu, kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya, kamar naman da za a sa a dafa.”

4 Sa’an nan za su kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa musu ba. A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su saboda irin muguntar da suka yi.

5 Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Game da annabawa masu ɓad da mutanena, in wani ya ciyar da su, sai su ce akwai ‘salama’ amma in bai ciyar da su ba, a shirye suke su kai masa hari.

6 Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba, kuma duhu, ba tare da duba ba. Rana za tă fāɗi wa annabawa, yini kuma zai zama musu duhu.

7 Masu gani za su ji kunya, masu duba kuma za su ji taƙaici. Dukansu za su rufe fuskokinsu gama ba amsa daga Allah.”

8 Amma game da ni, ina cike da iko ta wurin Ruhun Ubangiji da kuma adalci da ƙarfi, don a sanar da Yaƙub laifofinsa, ga Isra’ila kuma zunubinsa.

9 Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila, ku da kuke ƙyamar gaskiya, kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya;

10 kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini, Urushalima kuma ta wurin mugunta.

11 Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne, firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su, annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa, “Ba Ubangiji yana tare da mu ba? Ba bala’in da zai zo mana.”

12 Don haka, saboda ku, za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuma ta zama tarin juji, tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
Lean sinn:



Sanasan