Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Malaki 4 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Ranar Ubangiji

1 “Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

2 Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.

3 Sa’an nan za ku tattake mugaye; za su zama toka a ƙarƙashin tafin ƙafafunku a ranar da zan aikata waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji Maɗaukaki.

4 “Ku tuna da dokar bawana Musa, ƙa’idodi da dokokin da na ba shi a Horeb domin dukan Isra’ila.

5 “Ga shi, zan aika muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji tă zo.

6 Zai juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, zukatan ’ya’ya kuma ga iyayensu; in ba haka ba zan bugi ƙasar da hallaka gaba ɗaya.”

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
Lean sinn:



Sanasan