Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ƙidaya 29 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Bikin Ƙahoni
( Firistoci 23.23-25 )

1 “ ‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni.

2 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji, duka su kasance marasa lahani.

3 Tare da bijimin za a kuma miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;

4 kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.

5 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara.

6 Waɗannan ƙari ne ga hadayun ƙonawa na wata-wata da na kullayaumi, tare da hadayun garinsu da hadayun sha yadda aka tsara. Hadayu ne da aka miƙa wa Ubangiji ta wuta don daɗin ƙanshi.


Ranar Kafara
( Firistoci 23.26-32 )

7 “ ‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba.

8 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da kuma ’yan raguna bakwai, ’yan bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

9 Tare da bijimin a miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai;

10 kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.

11 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum; tare da hadaya ta garinta, da kuma hadayu na shansu.


Bikin tabanakul
( Firistoci 23.33-44 )

12 “ ‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai.

13 A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

14 Da kowane bijimai goma sha uku nan, a miƙa hadaya ta gari, kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da ragunan biyu ɗin, a miƙa hadaya ta gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai;

15 tare kuma da kowane ’yan raguna goma sha huɗu, kashi ɗaya bisa goma.

16 A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa na kullum tare da hadayarta, ta gari da kuma hadaya ta sha.

17 “ ‘A rana ta biyu, a miƙa bijimai goma sha biyu, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

18 Tare da bijiman, ragunan da ’yan ragunan a miƙa hadayarsu da gari da hadaya ta sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.

19 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya, don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadayunsu ta sha.

20 “ ‘A rana ta uku za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, raguna biyu, da kuma ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

21 Tare da bijiman, ragunan da ’yan raguna, a miƙa hadayun gari da hadayun sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.

22 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.

23 “ ‘A rana ta huɗu a miƙa bijimai goma, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

24 Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.

25 A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.

26 “ ‘A rana ta biyar a miƙa bijimai tara, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

27 Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayu na gari, da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.

28 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.

29 “ ‘A rana ta shida a miƙa bijimai takwas, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

30 Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu ta gari da hadayu na sha bisa adadin da a ƙayyade.

31 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadaya ta sha.

32 “ ‘A rana ta bakwai a miƙa bijimai bakwai, raguna biyu da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

33 Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari, da hadayun sha bisa ga adadin da a ƙayyade.

34 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.

35 “ ‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba.

36 A miƙa hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, a yi hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

37 Tare da bijimin, ragon da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.

38 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.

39 “ ‘Ban da abin da kuka yi alkawari, da kuma sadakokinku na yardar rai, a miƙa waɗannan ga Ubangiji a lokacin bukukkuwanku, hadayunku na ƙonawa, hadayu na gari, hadayu na sha da hadayu na salama.’ ”

40 Musa ya faɗa wa Isra’ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
Lean sinn:



Sanasan