Ishaya 4 - Sabon Rai Don Kowa 20201 A wannan rana mata guda bakwai za su cafke namiji guda su ce, “Ma ciyar da kanmu mu kuma yi wa kanmu sutura; ka dai bari mu ce kai ne mijinmu. Ka ɗauke mana kunyar da za mu sha.” Reshen Ubangiji 2 A wannan rana Reshen Ubangiji zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila. 3 Waɗanda suka rage a Sihiyona, waɗanda suka rage a Urushalima, za a ce da su masu tsarki, wato, dukan waɗanda aka rubuta a cikin masu rai a Urushalima. 4 Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta. 5 Sa’an nan Ubangiji zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa. 6 Za tă zama rumfa da inuwar da za tă tare zafin rana, da kuma mafaka da wurin ɓuya daga hadari da ruwan sama. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.