Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ishaya 35 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Farin cikin waɗanda aka ceta

1 Hamada da ƙeƙasasshiyar ƙasa za su yi murna; jeji zai yi farin ciki ya kuma hudo. Kamar fure,

2 zai buɗu ya hudo; zai yi farin ciki mai girma ya kuma yi sowa don farin ciki. Za a maido wa Lebanon da darajarta, darajar Karmel da Sharon; za su ga ɗaukakar Ubangiji, darajar Allahnmu.

3 Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi, ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji;

4 ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata, “Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro; Allahnku zai zo, zai zo domin ya ɗau fansa; da ramuwar Allah zai zo don yă cece ku.”

5 Sa’an nan idanun makafi za su buɗe kunnuwan kurame kuma su ji.

6 Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa, bebaye kuma su yi sowa don farin ciki. Ruwa zai kwararo daga jeji rafuffuka kuma a cikin hamada.

7 Yashi mai ƙuna zai zama tafki, ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka. A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama, ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma.

8 Kuma babbar hanya za tă kasance a can; za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki. Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba; za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce; mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba.

9 Zaki ba zai kasance a can ba, balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta; ba za a same su a can ba. Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can,

10 kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
Lean sinn:



Sanasan