Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ishaya 25 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Yabo ga Ubangiji

1 Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka, gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki, abubuwan da aka shirya tun da.

2 Ka mai da birnin tsibin tarkace, ka lalatar da gari mai katanga, birnin baƙi mai ƙarfi, ta ɓace; ba za a ƙara gina ta ba.

3 Saboda haka mutane masu ƙarfi za su girmama ka; biranen mugayen al’ummai za su ji tsoronka.

4 Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa, wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana. Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango

5 kuma kamar zafin hamada. Ka kwantar da hayaniyar baƙi; kamar yadda inuwar girgije kan rage zafin rana, haka ake kwantar da waƙar mugaye.

6 A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane, liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau.

7 A wannan dutse zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane, ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;

8 zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.

9 A wannan rana za su ce, “Tabbatacce wannan shi ne Allah; mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu. Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi; bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”

10 Hannun Ubangiji zai zauna a kan wannan dutse; amma za a tattake Mowab a ƙarƙashinsa kamar yadda ake tattaka kara a cikin taki.

11 Za su buɗe hannuwansa a cikinsa, yadda mai iyo kan buɗe hannuwansa don yă yi iyo. Allah ya ƙasƙantar da girmankansu duk da wayon hannuwansu.

12 Zai rurrushe manyan katangar kagaru ya kuma ƙasƙantar da su; zai rushe su har ƙasa, su zama ƙura.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
Lean sinn:



Sanasan