Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ishaya 20 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Annabci a kan Masar da Kush

1 A shekarar da babban shugaban yaƙin da Sargon sarkin Assuriya ya aika, ya zo Ashdod ya kuma fāɗa mata ya kuma ci ta da yaƙi,

2 a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.

3 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,

4 haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.

5 Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya.

6 A wannan rana mutanen da suke zama a bakin teku za su ce, ‘Dubi abin da ya faru da waɗanda muka dogara a kai, waɗanda muka gudu muka je don neman taimako da ceto daga sarkin Assuriya! Yaya za mu tsira?’ ”

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
Lean sinn:



Sanasan