Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Hosiya 14 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Tuba don kawo albarka

1 Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku. Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku!

2 Ku ɗauki magana tare da ku ku komo wurin Ubangiji. Ku ce masa, “Ka gafarta mana dukan zunubanmu ka kuma karɓe mu da alheri, don mu iya yabe ka da leɓunanmu.

3 Assuriya ba za su iya cece mu ba; ba za mu hau dawakan yaƙi ba. Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’ wa abin da hannuwanmu suka yi ba, gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.”

4 “Zan gyara ɓatancinsu in kuma ƙaunace su a sake, gama fushina ya juya daga gare su.

5 Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila zai yi fure kamar lili. Kamar al’ul na Lebanon zai sa saiwarsa zuwa ƙasa;

6 tohonsa za su yi girma. Darajarsa za tă zama kamar itacen zaitun, ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon.

7 Mutane za su sāke zauna a inuwarsa. Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi. Zai yi fure kamar kuringa, zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.

8 Efraim zai ce, me kuma zai haɗa ni da gumaka? Zan amsa masa in kuma lura da shi. Ni kamar koren itacen fir ne; amincinka yana fitowa daga gare ni ne.”

9 Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa. Hanyoyin Ubangiji daidai ne; masu adalci sukan yi tafiya a kansu, amma ’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
Lean sinn:



Sanasan