Esta 10 - Sabon Rai Don Kowa 2020Girman Mordekai 1 Sarki Zerzes ya sa a biya haraji a ko’ina a cikin daular, har zuwa ƙasashe masu nesa na bakin teku. 2 Dukan ayyukan Sarki Zerzes masu iko da masu girma tare da cikakken rahoton girmama Mordekai wanda sarki ya yi masa, ba a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Mediya da na Farisa ba? 3 Mordekai mutumin Yahuda, shi ne na biyu a matsayi bayan Sarki Zerzes, mai farin ciki kuma a cikin Yahudawa, aka kuma ɗauke shi da martaba cikin ’yan’uwansa Yahudawa. Gama ya yi aiki don kyautatawar mutanensa, ya kuma yi magana don a kyautata rayuwar dukan Yahudawa. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.