Ayuba 25 - Sabon Rai Don Kowa 2020Bildad 1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, 2 “Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa; yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama. 3 Za a iya ƙirga rundunarsa? A kan wane ne ba ya haska haskensa? 4 Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki? 5 In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa, 6 mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah!” |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.