Zabura 99 - Littafi Mai TsarkiAmincin Allah ga Isra'ila 1 Ubangiji Sarki ne, Mutane suna rawar jiki, Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi, Duniya ta girgiza. 2 Ubangiji mai iko ne a Sihiyona, Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al'umma. 3 Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki, Mai Tsarki ne shi! 4 Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai, Ka kawo adalci cikin Isra'ila, Ka kawo adalci da gaskiya. 5 Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a gaban kursiyinsa! Mai Tsarki ne shi! 6 Musa da Haruna firistocinsa ne, Sama'ila kuma mai yi masa sujada ne. Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu. 7 Ya yi magana da su daga girgije, Suka yi biyayya da dokoki da umarnai da ya ba su. 8 Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa wa jama'arka, Ka nuna musu, kai Allah ne mai yin gafara, Amma kakan hukunta su saboda zunubansu. 9 Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki! Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria