Zabura 98 - Littafi Mai TsarkiYabo saboda Adalcin Allah 1 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji, Gama ya aikata ayyuka masu banmamaki! Ta wurin ikonsa, da ƙarfinsa mai tsarki ya yi nasara. 2 Ubangiji ya bayyana cin nasararsa, Ya sanar da ikonsa na ceto ga sauran al'umma. 3 Ya cika alkawarinsa wanda ya yi wa jama'ar Isra'ila, Da tabbatacciyar ƙauna da aminci. Dukan mutane ko'ina sun ga nasarar Allahnmu! 4 Ku raira waƙa ta farin ciki ga Ubangiji. Dukanku waɗanda suke a duniya, Ku yabe shi da waƙoƙi, kuna ta da murya da ƙarfi, Saboda farin ciki! 5 Ku raira yabbai ga Ubangiji da garayu, Ku kaɗa garayu! 6 Ku busa kakaki da ƙahoni, Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, Sarki! 7 Ki yi ruri, ya ke teku, Ke da dukan masu rai waɗanda suke cikinki, Ki raira waƙa, ke duniya, Da dukan waɗanda suke zaune cikinki! 8 Ku yi tāfi, ya ku tekuna, Ku raira waƙa tare, ya ku tuddai, don farin ciki. 9 A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya yi mulki bisa duniya! Zai yi mulki bisa dukan jama'ar duniya da adalci da gaskiya. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria