Zabura 93 - Littafi Mai TsarkiAllah Sarki Ne 1 Ubangiji sarki ne! Yana saye da ɗaukaka, suturarsa ƙarfi ne. Hakika duniya ta kahu sosai a inda take, Ba kuwa za ta jijjigu ba. 2 Kursiyinka, ya Ubangiji, ya kahu tun daga farko, Kana nan tun fil azal. 3 Ya Ubangiji, zurfafan teku suna ta da muryarsu, Suna ta da muryarsu da ruri. 4 Ubangiji yana mulki cikin Sama, Mulkinsa mafifici ne, Fiye da rurin teku, Fiye da ikon raƙuman ruwan teku. 5 Dokokinka dawwamammu ne, ya Ubangiji, Haikalinka kuwa tsattsarka ne ƙwarai, Har abada abadin. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria