Zabura 87 - Littafi Mai TsarkiFa'idar Zama a Urushalima 1 Allah ya gina birninsa a bisa tsarkakan tuddai, 2 Yana ƙaunar birnin Urushalima fiye da kowane wuri a Isra'ila. 3 Ya birnin Allah, ka kasa kunne, Ga abubuwan banmamaki da ya faɗa a kanka. 4 “Sa'ad da na lasafta sauran al'umma da suke yi mini biyayya, Zan sa Masar da Babila a cikinsu, Zan ce da Filistiya, da Taya, da Habasha, Su ma na Urushalima ne.” 5 A kan Sihiyona kuwa za a ce, “Dukan sauran al'umma nata ne.” Maɗaukaki kuwa zai ƙarfafa ta. 6 Ubangiji zai rubuta lissafin jama'o'i, Ya sa su duka cikin jimilla ta Urushalima. 7 Duk mazauna a wurin za su raira waƙa, su yi rawa, Su ce, “Dukan maɓuɓɓugaina suna cikinka.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria