Zabura 8 - Littafi Mai TsarkiƊaukakar Allah da Martabar Mutum 1 Ya Ubangiji, Ubangijinmu, An san girmanka ko'ina a dukan duniya. Yabonka ya kai har sammai, 2 Yara da jarirai suna raira shi, Ka gina kagara saboda magabtanka, Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka. 3 Sa'ad da na duba sararin sama, wanda ka yi, Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu, 4 Wane ne mutum, har da kake tunawa da shi, Mutum kurum, har da kake lura da shi? 5 Duk da haka in banda kai ba wanda ya fi shi, Ka naɗa shi da daraja da girma! 6 Ka sa shi ya yi mulkin dukan abin da ka halitta, Ka ɗora shi a kan dukan abubuwa, 7 Tumaki da shanu, har ma da namomin jeji, 8 Da tsuntsaye da kifaye, Da dukan halittar da suke cikin tekuna. 9 Ya Ubangiji, Ubangijinmu, An san girmanka ko'ina a dukan duniya! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria