Zabura 61 - Littafi Mai TsarkiDogara ga Kiyayewar Allah 1 Ya Allah, ka ji kukana, Ka ji addu'ata! 2 Sa'ad da nake nesa da gida, zuciyata ta karai, Zan yi kira gare ka! Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka. 3 Kai ne kāriyata mai ƙarfi Da take kiyaye ni daga maƙiyana. 4 Ka yarda in zauna a alfarwarka dukan kwanakin raina, Ka yarda in sami zaman lafiya a ƙarƙashin fikafikanka. 5 Ya Allah, kā ji alkawaraina, Kā kuwa ba ni abin da ya dace, Tare da waɗanda suke ɗaukaka ka. 6 Ka ƙara wa sarki tsawon rai, Ka sa ya rayu dukan lokaci! 7 Ka sa ya yi mulki har abada a gabanka, ya Allah, Ka tsare shi da madawwamiyar ƙaunarka, da amincinka. 8 Don haka zan yi ta raira waƙar yabonka kullayaumin, A sa'ad da nake miƙa maka abin da na alkawarta. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria