Zabura 6 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Jinƙai a Lokacin Wahala 1 Ya Ubangiji, kada ka yi fushi, ka kuma tsauta mini! Kada ka hukunta ni da fushinka! 2 Ka ji tausayina, gama na gaji tiƙis, Ka wartsarkar da ni, gama na tafke sarai. 3 Duk na damu ƙwarai da gaske. Sai yaushe wannan zai ƙare, ya Ubangiji? 4 Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni, Gama kana ƙaunata, ka kuɓutar da ni daga mutuwa. 5 Ba za a tuna da kai a lahira ba, Ba wanda zai yabe ka a can! 6 Na gaji tiƙis saboda baƙin ciki, Kowane dare gadona yakan jiƙe saboda kukana. Matashin kaina ya yi sharkaf da hawaye. 7 Idanuna sun yi kumburi saboda yawan kuka, Har da ƙyar nake iya gani, Duk kuwa saboda abokan gābana! 8 Ku tafi daga nan, ku masu aikin mugunta! Ubangiji yana jin kukana. 9 Yana kasa kunne ga kukana na neman taimako, Yana kuwa amsa addu'o'ina. 10 Abokan gābana duka za su sha kunyar fāɗuwarsu, Suna cikin matsanancin ruɗami, Za a kwashe su farat ɗaya. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria