Zabura 57 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Kuɓuta daga Tsanani ( Zab 108.1-5 ) 1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi jinƙai, Gama na zo gare ka neman tsira. Zan sami kāriya a ƙarƙashin fikafikanka, Sai dukan hatsari ya wuce. 2 Zan yi kira ga Allah, Maɗaukaki, Zan yi kira ga Allah, mai biyan dukan bukatata. 3 Daga sammai Allah zai amsa mini, Zai kori waɗanda suka tasar mini, Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa. 4 Raina yana tsakiyar zakoki, Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane. Haƙoransu kamar māsu da kibau suke, Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi. 5 Ka bayyana girmanka ya Allah, a sararin sama, Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya! 6 Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni, Damuwa ta fi ƙarfina. Sun yi wushefe a kan hanyata, Amma su da kansu suka fāɗa a ciki. 7 A shirye nake, ya Allah, Na shirya sosai! Zan raira waƙoƙi in yabe ka! 8 Ka farka, ya raina! Ku farka, molona da garayata! Zan sa rana ta farka! 9 Zan gode maka a cikin sauran al'umma, ya Ubangiji! Zan yabe ka a cikin jama'a! 10 Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har sammai, Amincinka kuma har sararin sammai. 11 Ka bayyana girmanka, ya Allah, a sararin sama, Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria