Zabura 54 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Tsari daga Maƙiyi 1 Ka cece ni ta wurin ikonka, ya Allah, Ka cece ni ta wurin ƙarfinka! 2 Ka ji addu'ata, ya Allah, Ka saurari kalmomina! 3 Masu girmankai sun tasar mini, Mugaye suna nema su kashe ni, Mutanen da ba su kula da Allah ba. 4 Na sani Allah ne mai taimakona, Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona! 5 Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu! Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne. 6 Da murna zan miƙa maka hadaya, Zan yi maka godiya, ya Ubangiji, Domin kai mai alheri ne. 7 Ka cece ni daga dukan wahalaina, Na kuwa ga an kori maƙiyana. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria