Zabura 53 - Littafi Mai TsarkiMuguntar Mutane ( Zab 14.1-7 ) 1 Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah.” Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al'amura, Ba wanda yake aikata abin da yake daidai. 2 Daga Sama Allah ya dubi mutane, Ya ga ko akwai masu hikima Waɗanda suke yi masa sujada. 3 Amma dukansu sun koma baya, Su duka mugaye ne, Ba wanda yake aikata abin da yake daidai, Babu ko ɗaya. 4 Allah ya ce, “Ashe, ba su sani ba? Ashe, mugayen nan jahilai ne? Ta wurin yi wa jama'ata fashi suke rayuwa, Ba sa yin addu'a gare ni.” 5 Amma sa'an nan za su firgita ƙwarai, Irin yadda ba su taɓa yi ba, Gama Allah ya warwatsa ƙasusuwan maƙiyanka. Ya kore su sarai, saboda ya ƙi su. 6 Dā ma ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona! Sa'ad da Allah ya sāke arzuta jama'arsa, Zuriyar Yakubu za ta yi farin ciki, Jama'ar Isra'ila kuwa za ta yi murna. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria