Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Zabura 43 - Littafi Mai Tsarki


Addu'ar Wanda Aka Kai Baƙuwar Ƙasa ala Tilas

1 Ya Allah, ka kuɓutar da ni, Ka kiyaye al'amarina daga marasa tsoronka, Ka cece ni daga ƙaryar mugaye!

2 Ya Allah, kai ne kake kāre ni, Me ya sa ka yashe ni? Me ya sa nake ta shan wahala saboda muguntar maƙiyana?

3 Ka aiko da haskenka, da gaskiyarka, Bari su bishe ni, Su kawo ni Sihiyona, tsattsarkan tudunka, Su kawo ni Haikalinka, inda zatinka yake!

4 Sa'an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah, Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki, In raira waƙar yabo a gare ka da garayata, Ya Allah, Allahna!

5 Me ya sa nake baƙin ciki? Me ya sa nake damuwa? Zan dogara ga Allah, Zan ƙara yabonsa, Mai Cetona, Allahna.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan