Zabura 3 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Safe ta Dogara ga Allah 1 Ina da maƙiya da yawa, ya Ubangiji, Da yawa kuma sun juya, suna gāba da ni! 2 Suna magana a kaina, suna cewa, “Allah ba zai taimake shi ba!” 3 Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari, Kana ba ni nasara, Kana kuma maido mini da ƙarfin halina. 4 Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako, Ya kuwa amsa mini daga tsattsarkan dutsensa. 5 Na kwanta na yi barci, Na kuwa tashi lafiya lau, Gama Ubangiji yana kiyaye ni. 6 Ba na jin tsoron dubban abokan gāba Waɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe. 7 Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka yi nasara a kan dukan abokan gābana, Ka hallakar da dukan mugaye. 8 Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji, Bari yă sa wa jama'arsa albarka! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria