Zabura 26 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Tsare Mutunci 1 Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji, Gama na yi abin da suke daidai, Na dogara gare ka gaba ɗaya. 2 Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji, Ka gwada muradina da tunanina. 3 Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni, Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin. 4 Ba na tarayya da mutanen banza, Ba abin da ya gama ni da masu riya. 5 Ina ƙin tarayya da masu mugunta, Nakan kauce wa mugaye. 6 Ya Ubangiji, na wanke hannuwana Don in nuna ba ni da laifi, Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka. 7 Na raira waƙar godiya, Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki. 8 Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake, Inda ɗaukakarka yake zaune. 9 Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi, Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai, 10 Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci, A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa. 11 Amma ni, ina yin abin da yake daidai, Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni! 12 Na kuɓuta daga dukan hatsarori, A taron sujada na yabi Ubangiji! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria