Zabura 23 - Littafi Mai TsarkiUbangiji Makiyayina Ne 1 Ubangiji makiyayina ne, Ba zan rasa kome ba. 2 Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa, Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif. 3 Yana ba ni sabon ƙarfi. Yana bi da ni a hanyar da suke daidai kamar yadda ya alkawarta. 4 Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa, Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji, Gama kana tare da ni! Sandanka na makiyayi da kerenka Suna kiyaye lafiyata. 5 Ka shirya mini liyafa Inda maƙiyana duk za su iya ganina, Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai, Ka cika tanduna fal da mai. 6 Hakika, alherinka da ƙaunarka Za su kasance tare da ni muddin raina. Haikalinka zai zama gidana har abada. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria