Zabura 150 - Littafi Mai TsarkiKu Yabi Ubangiji 1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku yabi Allah a cikin Haikalinsa! Ku yabi ƙarfinsa a sama! 2 Ku yabe shi saboda manyan abubuwa Waɗanda ya aikata! Ku yabi mafificin girmansa! 3 Ku yabe shi da kakaki! Ku yabe shi da garayu da molaye! 4 Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa! Ku yabe shi da garayu da sarewa! 5 Ku yabe shi da kuge! Ku yabe shi da kuge masu amo! 6 Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai. Yabo ya tabbata ga Ubangiji! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria