Zabura 149 - Littafi Mai TsarkiBari Isra'ilawa su Yabi Ubangiji 1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji Ku yabe shi cikin taron jama'arsa masu aminci! 2 Ki yi murna, ke Isra'ila, sabili da Mahaliccinki, Ku yi farin ciki, ku jama'ar Sihiyona, sabili da Sarkinku! 3 Ku yabi sunansa, kuna taka rawa, Ku kaɗa bandiri da garayu, kuna yabonsa. 4 Ubangiji yana jin daɗin jama'arsa, Yakan girmama mai tawali'u ya sa ya ci nasara. 5 Bari jama'ar Allah su yi farin ciki saboda cin nasararsu, Su raira waƙa don farin ciki. 6 Bari su yi sowa da ƙarfi Sa'ad da suke yabon Allah, da takubansu masu kaifi. 7 Don su ci nasara bisa al'ummai, Su kuma hukunta wa jama'a, 8 Su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi, Su ɗaure shugabanninsu da sarƙoƙin baƙin ƙarfe, 9 Su hukunta wa al'ummai, kamar yadda Allah ya umarta. Wannan shi ne cin nasarar jama'ar Allah! Yabo ya tabbata ga Ubangiji! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria