Zabura 142 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Taimako 1 Ina kira ga Ubangiji don neman taimako, Ina roƙonsa. 2 Na kawo masa dukan koke-kokena, Na faɗa masa dukan wahalaina. 3 Sa'ad da na yi niyyar fid da zuciya, Ya san abin da zan yi. A kan hanyar da zan bi Maƙiyana sun kafa mini tarko a ɓoye. 4 Na duba kewaye da ni, sai na ga ba ni da wanda zai taimake ni, Ba wanda zai kiyaye ni, Ba kuwa wanda ya kula da ni. 5 Ya Ubangiji, na kawo kuka gare ka na neman taimako, Ya Ubangiji, kai ne mai kiyaye ni, Kai kaɗai nake so a rayuwata duka. 6 Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako, Gama na nutsa cikin fid da zuciya. Ka cece ni daga maƙiyana Waɗanda suka fi ƙarfina. 7 Ka cece ni daga cikin wahalata, Sa'an nan zan yabe ka cikin taron jama'arka, Domin ka yi mini alheri. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria