Zabura 141 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Maraice ta Neman Keɓewa daga Mugunta 1 Ina kira gare ka, ya Ubangiji, Ka taimake ni yanzu! Ka saurare ni sa'ad da na kira gare ka. 2 Ka karɓi addu'ata kamar turaren ƙonawa, Ka karɓi ɗaga hannuwa sama da na yi kamar hadayar maraice. 3 Ya Ubangiji, ka sa a yi tsaron bakina, Ka sa mai tsaro a leɓunana. 4 Ka tsare ni daga son yin mugunta, Ko kuma in haɗa kai da mugaye cikin muguntarsu, Ka sa kada in taɓa yin tarayya da su a bukukuwansu! 5 Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri, Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai, Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka. 6 Mutane za su yarda, cewa maganata gaskiya ce, Sa'ad da aka jefo da masu mulkinsu ƙasa, daga ƙwanƙolin dutse, 7 Kamar itacen da aka faskare, aka daddatse, Haka aka watsar da ƙasusuwansu a gefen kabari. 8 Amma ni, ya Ubangiji Allah, da nake dogara a gare ka, Ina neman kiyayewarka, Kada ka bar ni in halaka! 9 Ka kiyaye ni daga tarkunan da suka kafa mini, Daga ashiftar masu aikata mugunta. 10 Ka sa mugaye su fāɗa cikin tarkunansu, Ni kuwa in zo in wuce lafiya. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria